Za a Sa Noma a Muhimman Darusan Makarantun Sakandaren Najeriya

'Yan majalisa

Majalisar Dokokin Kasa ta shirya wata doka da za ta sa ilimin aikin noma ya zama muhimmin darasi a manhajar makarantun sakandare a Najeriya, kamar yadda darasin lisafi da harshen turanci su ke.

An kwashi shekaru ana bibiyan yadda za a inganta harkar noma saboda a samu wadataccen abinci a kasar da yadda yanzu haka matasa da dama suna kyamar aikin noma maimakon su rungume shi a matsayin sana'a.

Wannan ita ce hujjar da majalisa ta yi amfani da ita wajen amincewa da wannan dokar.

Dan majalisar wakilai Yusuf Buba Yakub, daga mazabar Gombi da Hong ta Jihar Adamawa shi ne ya dauki nauyin kudurin. A bayaninsa. Ya ce, “Ya kamata idan tun suna kanana a koya musu noma. Kamar yadda ake tilasta lisafi, shi ma harkan noma ya zama tilas.”

A bangaren Majalisar Dattawa kuma, tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin kula da harkar noma, ya ba kudurin goyon baya inda yace idan aka tilasta noma, zai sa hankalin yara ya dawo kan harkar noma, su yi yadda iyayen iyayensu suka yi, su ga cewa ba abun gujewa ba ne.

Shi ma dan majalisar wakilai daga mazabar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe, Abubakar Yunusa Ahmed ya amince da cewa doka ce mai ma'ana.

To sai dai daya cikin matasan kasar, Mustapha Dauda, daga Jos, babban birnin jihar Filato, yana ganin kafin yanzu ana da makarantun koyar da aikin noma da yawa amma daliban ba sa samun aiki in sun kammala karatun.

Abin jira a gani shi ne ko majalisa za ta sake yin wata doka da za ta kebe wa kwararrun manoma guraben aiki da kuma samar masu kayan noma, lokaci ne kadai za tabbatar da haka.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Noma Zai Zama Darasin Tilas A Makarantun Sakandare A Najeriya - Majalisar Dokokin Kasa