Karancin man da ake fama dashi a kasar musamman a arewa yanzu ya kai wata biyu.
Kamfanin man fetur din wato NNPC na zargin cewa bayan an yi dakon man daga Legas ko Fatakwal zuwa arewacin kasar akan karkatashi zuwa wani wurin ko a boyeshi.
To saidai kungiyar dillalan man fetur ta mayarda da martani. Tace NNPC ta kasa kare matatun mai da depo depo nata da bututun mai sannan duk man da ake sayarwa a kasuwar bayan fage daga gidajen man NNPC din yake fitowa.
Mai magana da yawun kungiyar dillalan yace yana da gidajen mai a Kano sun fi dubu biyar amma idan za'a raba motoci goma sai a bashi biyar su kuma a basu biyar lamarin da yace babu adalci ciki.
Idan gwamnati zata wadatar da mai ta yi a gani. Idan kuma tana son ta shigar da siyasa ciki ta tuna cewa harkar tattalin arzikin kasa ba'a shigar da siyasa ciki, inji Alhaji Bashir Dan Malam shugaban kungiyar dillalan man fetur na kasa mai kula da shiyar Kano.
A wani halin kuma ofishin man fetur sashen dake kula da cinikayyar albarkatun man fetur wato DPR yace ya hukunta gidajen mai 39 saboda karya kai'dodin da aka shimfida masu.
Alhaji Isa Tafida babban jami'in DPR yace ana sayarwa dillalan mai akan kudi nera 76 su kuma su sayar akan nera 87 amma ba zasu sayar ba ido na ganin ido sai wajen karfe ukun dare su kwashe su sayarwa kasuwar bayan fage.
To amma dillalan sun kalubali zargin da DPR ta yi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5