NNPC: Shugaba Buhari Ya Gargadi Kamfanin Yayi Cudanya da 'Yan Kasa

Shugaba Muhammad Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya gargadi ma'aikatar man fetur din Najeriya ta yi aiki kafada da kafada da kamfanonin man fetur na 'yan kasa masu zaman kansu.

Shugaban na son NNPC ya dinga muamala ta kud da kud da kamfanonin 'yan Najeriya dake harkokin man fetur.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da shugabannin kamfanonin suka ziyarceshi inda suka yaba masa da irin matakan da yake dauka saboda farfado da ma'aikatar man fetur.

Shugaban ya dauki lokaci mai tsawo yana sauraran shugabannin kamfanonin masu shigo da man fetur da aikin harkokin iskar gas domin fahimtar bukatunsu da kuma irin matsalolin da suke fuskanta da kuma irin matakin da yakamata gwamnati ta dauka domin inganta aikinsu.

Shugaban yana son ya tabbatar an samu mai akasar ba tare da wata matsala ba kamar yadda ake cigaba da fuskanta lokaci zuwa lokaci akan samun mai.

Kungiyoyin suna fata zasu yi aiki da gwamnatin Buhari da nufi habbaka ayyukansu. Yakamata a duba a ga abun da shugaban yake so da kuma nasu bukatun saboda a san abun da za'a yi saboda kasar ta samu ta ci albarkatun man da take dashi..

Ga cikakken bayani

Your browser doesn’t support HTML5

NNPC: Shugaba Buhari Ya Gargadi Kamfanin Yayi Cudanya da 'Yan Kasa