NLC: Anya Babu Yaudara A Kwamitin Da Gwamnatin Tarayya Ta Kafa?

Kwamitin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa don karin albashin ma'aikata, ya fara aiki gadan gadan.

Aci gaba da murza gashin baki tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar 'yan kwadago ta NLC game da karin albashin ma’aikatan Najeriya.

A jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani kwamiti dake karkashin sanannen masanin tattalin arziki Mr Bishmak Riwane, wanda kuma aka debawa kwanaki 30 domin yin nazari da kuma mika rahoton karin na albashi.

A jawabinsa wajen kaddamar da wannan kwamitin, shugaba Buhari yace akwai bukatar yin garon bawul ga daukacin albashin ma’aikata, ko kuma dai dai ta su domin tafiya tare.

Tuni dai kungiyar kwadago ta kasa tayi fatali da wannan kwamitin, tana mai cewa, wata dabara ce ta gwamnati na jan kafa a dai dai lokacin da zaben kasa ya karato.

Ra’ayin wasu 'yan Najeriya game da shirin karin albashin ko akasin hakan ya banbanta. Wasu na ganin gaskiya mafi karancin albashi na Naira dubu goma sha takwas yayi kadan a kasar nan.

Shima wani malamin, cewa yayi akwai bukatar gwamnati ta kara albashin, domin biyan bukatun ma’aikata, waddanda ke zaune a gidajen haya ko biyan kudin makaranta yara ya za suyi? Ai ko sabon albashin na naira 30,000 sai maneji.

Sauda yawa dai wasu na ganin idan aka kara albashin, hakan zai haifar da tsadar kayan masarufi, hasashen da wani masanin tattalin arziki Malam Isa Imam, yace ba gaskiya bane; yace koda yake za’a samu karin farashin kaya, amma hakan ba zai taka kara ya karya ba, domin tashin kayan bazai dore ba kamar yadda ake gani a wasu kasashe da basu da karfin tattalin arziki.

Yanzu dai abun jira a gani shine ko rahoton da wannan kwamitin zai mikawa gwamnatin, ana saura mako daya zaben kasa, zai yi tasiri ga ma’aikatan na samun karin, kafun zaben kasa?

Ga rahoton wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Babangida Jibril.

Your browser doesn’t support HTML5

NLC: Anya Babu Yaudara A Kwamitin Da Gwamnatin Tarayya Ta Kafa? 3"10"