A karon farko Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi, ya fito baina jama’a, tun bayan wani yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar.
A yau Lahadi shugaban ya gaisa da manema labarai a Fadarsa da ke Bujumbura, babban birnin kasar.
A wani jawabi da ya yi ta kafar radio a ranar juma’ar da ta gabata, Nkurunziza ya mika godiyarsa ga jami’an tsaron kasar da suka dakile yunkurin juyin mulki da aka so a yiwa gwamnatinsa.
Ya kuma yi gargadi ga masu zanga zanga da su daina adawa da yunkurinsa na yin tazarce, wanda suka ce ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
Nkurunziza da magoya bayansa, suna ikrarin cewa ‘yan majalisar dokoki ne suka zabe shi a wa’adinsa na farko ba masu kada kuri’a ba.
Kotun kundin tsarin mulkin kasar dai ta amince shugaban ya sake tsayawa takara.