Nishadi Tare Da S. Imam

Nishadi Tare Da S. Imam

A shirin mu na nishadi yau mun sami bakuncin wani mawaki mai suna S. Imam wanda ke sana'ar waka, kuma ya bayyana mana cewa ya tsinci kansa a wannan sana'a ta waka koda shike ya ce ya fuskanci kalubale da dama.

Mawakin ya ce babu wanda ya taba koya masa waka, ra'ayi ne kawai da kuma sa kai, domin kuwa a cewar sa tun tana yaro karami yake shi'awar sauraron wakokin irin su Kirfi Usman M. Ahmed, Aminu Alan waka, da Dayyabu Mai Da'a da sauran su kuma suna burge shi kwarai, dan haka a takaice dai wadannan mawaka ne suka ja hankalin sa har ya fara raira wakoki.

A wata tambaya da wakilyar dandalin voa Baraka Bashir ta yi masa akan abubuwan da ke daukar hankalinsa har ya yi waka sai ya bada amsar cewa wasu wakokin da dama sukan fado masa a rai ne kawai ba tare da ya zauna ya tsara su ba, wasu kuma ana shi yayi ne wato misali irin wakokin siyasa.

Ga cikakkiyar hirar.