Kimanin ‘yan majalisa 115 daga kasashe 15 na yammacin Afrika ne suka yi rantsuwar kama aiki yau yayin bikin da shugaban rikon kungiyar Ecowas Issouhou Mahamadou na Nijer ya jagoranta a birnin Yamai.
Dan majalisar dokokin kasa Boukari Sani Zilly, na daga cikin masu wakiltar al’ummar Nijer a wannan sabuwar majalisa, ya yi kashedi ga duk masu neman yin katsalandaakan dokar dake cikin kungiysr.
Da yake jawabin bankwana shugaban majalisar mai barin gado Moustapha Cisse Lo, ya bayyana gamsuwa da irin aiyukan da majalisar ta Cedeao ta gudanar a tsawon shekaru 4 da suka gabata, duk da yake, bisa ga cewar shi har yanzu da sauran aiki.
Cissie ya ce "kamar yadda abin yake a jiya, a yau ma talakawa na jiran ganin an magance wasu tarin matsaloli da suka fi addabar su wato zaman lafiya tsaro ‘yanci, kwanciyar hankali da dimokradiyya sai uwa uba batun inganta rayuwar al’ummomi a daukacin kasashen".
A nasa jawabin shugaban rikon kungiyar Cedeao Issouhou Mahamadou na Nijer ya tabo wasu muhimman batutuwan da ke faruwa a wannan yanki a fannin siyasa a yanzu haka, inda yace an fara samun ci gaban dimokaradiyya. Shugaban yace “ina yaba wa dan'uwana Alassan outtara na kasar Cote d’Ivoire bayan da ya janye kudirin tazarcen da ya sa gaba a can baya. A saboda haka ina yin kira ga shugabannin Guinea Bissau da Guinea Conakry da su yi koyi da wannan kyakkyawan missali don kaucewa barkewar rigingimu".
Shugaban kasar Nijer ya kuma shawarci kasashen Afrika ta yamma da su gaggauta hada karfi karkashin inuwar kungiyar lafiyar yankin wato OAS don tunkarar cutar Coronavirus da ke kara yaduwa a sassan duniya.
Batun tsaro a yankin Sahel da yankin tafkin Chadi na daga cikin matsalolin da kungiyar Cedeao ke fadi tashin ganin ta magance kamar yadda yake rubuce a wata ajandar shekaru 4, saboda haka sabuwar majalisar dokokin dake matsayin na 5 a tarihin wannan yanki ke da alhakin bullo da shawarwari a karshen wannan zama na tsawon kwanaki 5.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5