Nijar Za Ta Kara Kaimi Wajen Yaki Da Safarar Mutane Da Miyagun Kwayoyi

Taron Alkalai

A cigaba da yaki da safarar mutane da muggan kwayoyi da ta ke yi, Janhuriyar Nijar ta lashi takobin ganin bayan masu aikata wadannan manyan laifuka a kasar.

Alkalai na manyan kotuna da na kotun daukaka kara na Janhuriyar Nijar na can su na ganawa a Birnin Agadez da ke arewacin kasar game da dokar nan mai takawa masu safarar bakin haure da fataucin miyagun kwayoyi.

Malam Sadu Saloke, shi ne gwamnan jahar Agadez a lokacin da ya ke jawabi a wurin bude taron na alkalai a garin na Agadez.

"Halartar ku a wurin wannan taron na kara mu na murna da jin dadi, hasali ma, ya na nuna muna irin yanda kuke girmama doka," in ji shi. A nata bangaren, shugabar ma'aikatar da ke yaki da safarar bil'adama da bakin haure da fataucin miyagun kwayoyi, ta bayyana irin gurin da hukumomin kasar ke son a cimma a karshen wannan taron na alkalan Nijer a Agadez.


Tun yan shekarun da suka gabata, offishin ministan shari'a na wannan kasar ya kawo sauyi domin yaki da safarar bil'adama da bakin haure da fataucin miyagun kwayoyi a wannan ko wancan iyakokin kasashen mu, kuma, a kan haka ne, offishin ministan shari'a ya mayar da hankali a kan yaki da ta'adanci, safarar bil'adama da bakin haure da yaki da fataucin miyagun kwayoyi.


Taron, zai dauki kwanaki 3 tareda halartar alakalai, hukumomin kasar, offishin majalisar dumkin duniya mai yaki da safarar bil'adama da bakin haure, da fataucin miyagun kwayoyi.

Ga wakilinmu Haruna Mamman Bako da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Za Ta Kara Kaimi Wajen Yaki Da Safarar Mutane