Nijar Za Ta Bullo Da Sabbin Dabarun Dakile Ayyukan 'Yan ta'adda - Bazoum

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyar Nijar wacce ke makwabtaka da Najeriya, ta jima tana fama da mayakan Boko Haram da ke kwararowa daga makwabciyar ta ta.
A Jamhuriyar Nijar, shugaba Mohamed Bazoum ya sha alwashin rufe hanyoyin da ‘yan ta’adda ke bi su shiga wasu wurare a yankin Tillaberi mai fama da ayyukan ‘yan bindiga. Shugaban ya sanar da hakan ne yayin wata ziyara da ya kai yankin na Tillaberi. Ga Yusuf Abdoulaye daga Yamai.