Kamar ko'ina a fadin duniya, jamhuriyar Nijar ba a barta a baya ba a yau 21 ga watan Fabrairu domin tunawa da ma waye kai da fadakarda al'ummar wannan kasar wajen muhimancin harshen uwa.
Malam Amadu Kane shi ne shugaban barikin koyarda halshen Hausa a gundumar Birni N'Konni ya ce wannan rana an kebeta domin kira ne ga al'umma da su san cewa harshen uwa yana da muhimmancin, kuma koyar da yara karatu da harshen uwa, yakan masu saukin koya.
Hukumomin jamhuriyar Nijar na cigaba da mayarda hankali a yan shekarun baya domin ganin cewa dalibai sun yi anfana da karatu ta hanyar harshen uwa domin kawo masu sauki wajen yin karatun boko, tare da korar jahilci da samun ilmin dogaro da rayuwa.
Wadansu daga cikin masu yin karatu, da koyarwa da harshen uwa, da aka tattauna dasu, sun nuna muhimancin koyan karatu a cikin harshen uwa.
A birane da karkara a jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar ne tare da kungiyoyi masu zaman kansu, da masu hannu da shuni dake dafawa kasar, ke cigaba da bada nasu kokari da tallafi domin ganin dattijai, tsofaffi da matasa, da yara dukkan su maza da mata sun yi karatu a cikin harsunan uwa.
Wannan yunkurin ne na yakar jalci da samun ilmi domin adama da su a cikin harkokin yau da kullum na wannan duniya da a kewa kirari tana a tafin hannu bisa la'akari da ilmi internet ko yanar gizo da ke baiwa jama'a sanin halinda duniya ke ciki a yan kankanan lokuta.
A saurari rahoto cikin sauti daga Birnin N'Konni a Jamhuriyar Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5