A wata takardar da ta aikewa shugabannin 'yan kasuwa hukumar dake kula da lamuran babbar kasuwar birnin Yamai ta sanar da karin kudin hayar shaguna da ta alakanta da komadar tattalin arziki.
Sai dai matakin hukumar ya bata wa 'yan kasuwan rai kuma sun sha alwashi ba zasu lamunta da shi ba. Sanadiyar hakan 'yan kasuwan sun rufe shagunansu a cikin kasuwar yau Litinin saboda karin ya yi yawa matuka.
Ibrahim Garba sakataren tsare tsare na kungiyar 'yan kasuwa yayi karin bayani. Yana mai cewa shagunan daban daban suke. Karin da aka yi ya shafi duka shagunan.Shagon da suke biyan jaka shida da 'yan kai da yanzu zasu biya jaka arba'in. Na jaka tara da dala casa'in da bakawai yanzu zasu biya jaka sittin. Na jaka goma sha biyu da rabi an ce su biya jaka tamanin.
Da jin wannan labarin ministan kasuwanci ya kira shugabannin 'yan kasuwan domin samun masalaha kan rikicin wanda tuni ya isa kotun sasanta rigingimun 'yan kasuwa.
Yayinda su 'yan kasuwan ke jiran jin bahasin ministan kasuwanci, sun ce idan alkali ya kirasu zasu bashi labarin abubuwan dake gudana.
Hukuma dake kula da kasuwar ita ma ta ruga kotun domin jiran ta fuskanci 'yan kasuwan.
To saidai wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kasuwan ke kukan rashin ciniki inji Bubakar Yusufu wanda shi ma dan kasuwa ne.
Yajin aikin ya yi tasiri akan harkokin yau da kullum kamar yadda wasu mazaunan Yamai suka shaida. Mutane da dama ne suka isa kasuwar domin sayen kaya amma basu samu ba.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5