Matashiyar mai suna Zara Umaru ta kafa wannan masana'anta da a cewar ta ta dauki matasa kimanin arba'in aiki yayin shirya wani fim mai sunan YANCI da ya hada kan matasa masu sana’ar fina finai ‘yan Jamhumiyar Nijar da Najeriya.
Yayin kaddamarwar, Zara ta yi kira ga gwmnan jihar Damagaram Lawli Madigu da ya jagoranci kaddamar da kamfanin da ya zame mata kafada da zata dafa ta tashi.
Gwamnan ya jinjina wa matashiyar da wannan hobbasa da ya kasance sabon abu ya kuma yi alkawarin kama mata don cikar burin ta na bunkasa al'adun kasar da samarwa matasa aiki, da kuma bunkasa tattalin arziki.
Taron ya samu halartar kungiyar shirya fina finai ta Kano MOFAN inda jagoran ta Ado Ahmed Gidan Dbino ya ce sun yaba da kokarin matashiyar na kafa kamfanin. Ya kuma yi alkawarin bata gudumuwa da shawarwari. Bisa ga cewar shi, tuni suka sanya hannu a wata yarjejeniya ta yin aiki tare tsakanin Nijar da Najeriya.
Suma ‘yan wasan fina finai na Nijar da Najeriya sun yi alkawarin bata goyon baya.
Saurari cikakken rahoton Tamar Abari cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5