Yayinda zaben gama gari na Jamhuriyar Nijar ke karatowa wasu jam'iyyu sun kulla kawance da zummar tsayar da dan takara daya a zabe mai zuwa
WASHINGTON DC —
Shugabannin jam'iyyun sun rabtaba hannu akan yarjejeniyar da suka yi da ya basu damar shiga zaben shugaban kasa da dan takara daya.
Kakakin 'yan adawa Husseini Talatu na cewa sun amince su marawa duk dankaran da yazo na biyu a zagayen farkon zaben shugaban kasa saboda bashi damar lashe zaben shugaban kasa..
Wadanda basu da dan takarar shugaban kasa sun amince su zabi dan takarar kawancen adawa tun a zagayen farko. Haka ma na zaben 'yan majalisar dokoki.
Sakataren jam'iyyar MNSD Nasara Tijjani Abdulkadiri ya bayyana cewa sun dauki duk matakan kaucewa rarrabuwar kawuna tsakaninsu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5