Ministan harkokin cikin gida a jamhuriyar Nijar Mal Bazum Mohammed, ya kai ziyara a jahar Tawa, inda a farkon wannan wata wasu 'yan bindiga da ake zargi sun fito daga makwabciyar kasar Mali, suka kai farmaki kan jami'an tsaron kasar da suke tsaro a wani sansanin 'yan gudun hijira daga Mali suke tsugune.
Suka kashe sojojin Nijar 22, suka jikkata wasu da dama. Amma basu taba 'yan gudun hijira ba.
Da yake magana kan wannan batu, Minista Bazum yace Nijar ta dauki matakai na inganta tsaro, biyo bayan wasu hare hare daban daban da 'yan ta'adda suka kai cikin kasar a baya bayan nan.
Ministan yayi ta'aziyya a madadin gwamnati da al'umar kasar ga iyalan wadanda wannan hari ya rutsa da su.
Shima da yake magana, Gwamnan jahar Tawa, Mal Abdulrahman, yace cikin matakan da gwamnati ta dauka na karfafa tsaro sun hada harda sayen motoci da kuma jirage masu saukar ungulu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5