Nijar Na Tattaunawa Kan Hanyoyin Tabbatar Da Ka'ida A Aikin Asibiti

  • Ibrahim Garba

Shugaban Nijar MUHAMMADOU ISSOUFOU

Janhuriyar Nijar na duba hanyoyi inganta tsari da kuma ka'idojin aikin asibiti da kuma asibitoci masu zaman kansu don amfanar jama'a.

A cigaba da inganta tsarin bangaren kiwon lafiya na Janhuriyar Nijar, musamman ma game da asibitoci masu zaman kansu da dakunan sayar da magunguna ko ‘kemis-kemis’ da kuma makarantun koyon aikin asibiti masu zaman kansu, Janhuriyar Nijar ta kira taron masu ruwa da tsaki don musayar ra’ayi da kuma duba hanyoyin inganta al’amura.

Ministan Lafiya na Janhuriyar Nijar, Dakta Idi Iliyasu Mainasara, y ace kamata ya yi a rinka aiki da yadda kundi ya tsara aikin kiwon lafiya saboda a kare marar lafiya. Ya ce bai kamata karamin likita ya yi fit aba musamman idan hakan zai hada da taba kayan ciki. Ministan y ace ya kamata shi kuma babban likita ya tausaya ma masu kananan karfi wajen ganin cewa ya yi komai ba don kudi kawai ba. Su kuma masu makarantun koyar da aikin asibiti ya kamata su tabbatar wadanda su ka cancanta ne ke koyarwa.

Ita ko Shugabar Kungiyar Ma’abuta Asibitoci masu zaman kansu Madam Kasim Hajiya Safiyatu ta yaba da irin matakan da hukumomin kiwon lafiya su ka dauka. To amma ta yi kiran da a rinka sassauci wajen aiwatar da kyawawan matakai wadanda su ke kuma da tsauri.

Ga dai wakilinmu a Yamai Sule Mummuni Baram da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Na Tattaunawa Kan Hanyoyin Tabbatar Da Ka'ida A Aikin Asibiti