Malaman jami'o'i na Jamhuriyar Nijar sun tsunduma yajin aikin na sai baba ta gani har tsawon wata guda a wani takun saka tsakaninsu da gwamnati da ta ki yarda da zaben jagororin jami'a da suke so a yi.
Tuni majalisar dokoki ta sanya hannu kan dokar cewa gwamnatin ce za ta nada su, a cewar Ministan Ilimi mai zurfi Yahuza Sadisu a wani taron manema labarai.
Abin da malaman suka ki, shine a cewarsu gwamnati tayi musu alkawarin da bata cika ba, a shekarar bara a wani zama da suka yi kan wannan matsalar inji Docta Ado Arifa Musa mataimakin magatakardar kungiyar malaman ta SNECS, inda ya ci gaba da cewa ba za su gushe daga hakan ba sai dai gwamnati ta yi ma dokar kwaskwarima, ba wai sun ce a soke ta ba.
Game da kudaden da suka ce suna bin gwamnati na wasu hakkokinsu, Ministan ya ce kimanin million 800 da 'yan kai ne, wanda suka shafi jami'o'in Yamai, Tawa da Agadez, yayin da na Damagaram, Diffa,Tillbery, da Maradi ba su bin su, za su biya su ba da jimawa ba.
Su kuma dilibai suna fargaba, ganin shekarar bara ma haka ta salwance sabili da wannan matsala ta yajin aikin malamai.
A saurari rahoto cikin sauti daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.
Your browser doesn’t support HTML5