A Jamhuriyar Nijar kungiyar jami’an kwastam ta koka da nadin da gwamnatin kasar ta yi wa wani jami’in da ta ce ba na kwastam ba domin ya shugabanci hukumar kasar.
WASHINGTON D.C. —
Matakin nadin ya zo ne a wani lokaci da gwamnatin ta Nijar ta bukaci jami’an na kwastam da na haraji su kara matsa kaimi don samar da kudaden shiga a aljihunta.
Kungiyar ta bayyana wannan korafi na ta ne a wani taron da ta kira domin ta fadi halin da ta ke ciki.
Kungiyar ta yi ikrarin cewa wanda aka nada, Janar Amadu Halidu, ba shi da kwarewar da zai jagoranci hukumar.
A taron majalisar zartarwar kasar da aka yi a baya-baya nan wanda shugaba Muhammadu Isuhu ya jagoranta aka tabbatarwa da Halidu wannan mukami.
Domin jin cikakken rahoton, saurari wakilinmu Sule Mumuni Barma da ya hada mana wannan rahoto daga birnin Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5