Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijer HALCIA da kungiyar tallafawa kasashe masu tasowa ta kasar Jamus GIZ, sun kaddamar da wani shiri a Birnin N'Konni na yiwa jama'a takardun shige da fice na kasashen ECOWAS ko CEDEAO.
WASHINGTON D.C —
Malam Isufu Abdullahi shine ke jagoran wannan aikin dake wakana a cikin ma'aikatar magajin garin Birni N'Konni, inda yanzu haka mutane kimanin 750 a birnin da kauyukan za su samu wannan takarda da za ta basu damar ketarawa kasashen ECOWAS.
Mutane da dama sun koka game da irin yadda suke fuskantar matsalolin akan iyakokin kasashe CEDEAO ko ECOWAS a lokacin da suke balaguro, ya yin da yakan kai su da dole su bada na goro kamin abar su, su shiga wasu kasashen yankin ECOWAS.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta bayyana jin dadin ta game da wannan shirin kuma sun yi maraba dashi domin zai taimaka wajen inganta tsaron shiga da fice Iyakokin kasashen ECOWAS.
Saurari Rahoton Harouna Mamane Bako
Your browser doesn’t support HTML5