Leftanar Janar Tukur Buratai, babban hafsan mayakan kasa na Najeriya shine ya tabbatar da haka, yace tuni kasashen biyu suke aiki ta fuskar difilomasiyya data soja domin magance kutsen da 'yan binidga suke yi kan iyakokin kasshen biyu.
Idan za'a iya tunawa a shirin ranar Alhamis, Ministan tsaron jamhuriyar Nijar Kalla Moutari, yace dakarun kasshen biyu suna aiki tare ta wajen yin sintiri, domin magance 'yan binidgar masu neman kafa gindin zama akan iyakar kasar, watakil ganin yadda farmaki daga dakarun Najeriya ka iya korarsu su nemi tsallakawa zuwa Nijar.
Shima da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu,tsohon Gwamnan soja a jihohin kano da Benue,kanal Aminu Isa kontagora yace akwai bukatar a fadada rundunonin soja da suke aiki a jihohi da suke kan iyaka.
Shugaban hukumar wayar da kan al'uma ta Najeriya Dr. Garba Abari, yayi kira da jama'a su baiwa jami'an tsaro hadin kai domin a sami nasarar kawar da batagari.
Ga rahoton Hassan Maina kaina.
Your browser doesn’t support HTML5