NIJAR: An Kafa Dokar Sa Hullar Kwano A Jihar Agadez

NIGER: Diffa ta hana hawan babura

Jahar Agadez dake arewacin Nijar tabi sahun babban Birnin Yamai tareda kasancewa ta 2 bayan hedkwatar kasar wajen daukar dokar tilasa masu hawan babura sa hullar kwano, yayin da masu Shiga mota, zai kasance musu wajibi da su sa igiyar kariya ko sit bel da a ke kira sintir de sekurite da faransanci.

Dokar, zata soma aiki ne, a ranar 9 watan Nuwamba mai zuwa ne Birnin Agadez kuma, duk wanda aka kama bisa babur ba hullar kwano ko cikin mota ba igiyar kariya zai fuskanci fushin hukuma.

An kafa dokar ne da nufin rage mace macen matafiya a hadura da kuma kara fargar da al’umma kan daukar matakan kariya da kiyaye dokokin tuki.

Mutanen da Sashen Hausa ya yi hira da su sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi dangane da batun, yayinda suke fatar wannan dokar zata taimaka wajen shawo kan matsalar ganganci a ayyukan sufuri.

Saurari cikakken rahoton Haruna Mamman Bako

Your browser doesn’t support HTML5

Dokar Sa Hular Kwano a Agadez-2:20"