Shugaban Majalisar Mai Tangale Abdu Buba Sharu ya gana da manema labarai a fadarsa dake garin Billiri a jihar Gombe.
Ya shaidawa 'yn jarida abubuwan da suka tattauna yayinda suke ziyarar. Kafin ya soma bayani ya bukaci addu'o'i ma shugaban kasa da gwamnoni saboda su samu nasara akan ayyukan da suka sa gabansu.
Mai Tangale yace a tashi manufar a yiwa shugaban kasa addu'a saboda aikin dake gabansa. A halin da ake ciki yanzu babu wanda zai ce abubuwa basu fara yin kyau ba. Saboda haka sai a kara sashi cikin addu'a.
Sun fara kai ziyarsu da zuwa ganin gwamnan Kaduna Malam Nasiru Rufa'i Yace zuwansu ya yi kyau. Sun yi magana da gwamnan basu kuma boye masa komi ba. A ganinsu idan an kiyaye wasu abubuwa za'a samu fahimtar juna kuma a samu hadin kai tsakanin Kiristoci da 'yanuwa Musulmi.
Daga Kaduna sai Kano inda suka gana da mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi wanda suka ce sun san yana son zaman lafiya. Sun fada masa manufar zuwansu na son a zauna lafiya tsakanin kirista da musulmi tare da wadanda suke addinin gargajiya a kasar. Rashin zaman lafiya a arewa yana shafar yankin ainun.
Rashin zaman lafiya ya kara sa yankin komawa baya. Dama yankin yana da koma baya kan ilimi da masana'antu sai kuma gashi rigingimun yankin ya sa an rufe makarantu a wurare da dama. Wadan nan abubuwa sun maida matasa baya. Dalili ke nan hankalinsu ya tashi. Sun samu damuwa.
A koma shirin da can lokacin da kirista da musulmi ke zaman lafiya da juna.Yace a dukufa da yin addu'a tare da tsawaitawa wadanda suka tada zaune tsaye.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5