Majalisar zartaswar Nigeria ta amince da karbo lamunin dalar Amurka miliyan 150 daga bankin duniya a kokarinta na ci gaba da yaki da cutar polio.
Har yanzu ana fama da cutar polio a Nigeria sanadiyar kin amincewa da allurar rigakafi da wasu iyayen yara ke yi, da kuma matsalolin tsaro lamuran dake kawowa hukumomin kiwon lafiyar kasa cikas a wurin yaki da cutar polio.
A baya bayan nan kasar ta shawo kan matasalar ta hanyar wayar da kawunan jama'a da kuma jaddada mahimmancin rigakafin.
Wasu iyaye da aka zanta dasu sun bayyana irin kokarin da suka yi.Malam Umar Faruk ya ce yana da mata biyu kuma ko yaushe ya bar gida ya kan fada masu da zara an zo ba da allurar rigkafin polio su tabbata sun mika 'ya'yansu an yi masu.
Ita ko Jamila Bello cewa ta yi duk wadanda ba sa kai 'ya'yansu a basu allurar yakamata a nanata masu su rika kai yaransu saboda idan basu kaisu ba suna haduwa da yaran da suka samu allurar a makaranata, cikin unguwanni da wurin wasa. Cututukan da wadanda basu da allurar ke dashi na iya sahafar wadanda suka karbi allurar.
Wani ya bada shawarar cewa idan ana so a shawo kan wannan matsala, tilas ne a yi anfani da shugabannin al'umma da na addini, domin a shawo kawunan iyayen da har yanzu basu yadda da allurar ba.
A saurari rahoton Hauwa Umar domin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5