Kama daga shugabannin kasar zuwa talakawa duk rububi su keyi wajen sayen kayan da aka sarafa a kasashen ketare.
Abubuwan da suke rububin saye sun kama ne daga tsinken sakace zuwa su sabulun wanka da kayan hawa da kuma na kawa.
Dogaro kan kayan da aka sarafasu a ketare ba karamin illa yake yiwa tattalin arziki ba lamarin da ya sa yanzu sabuwar gwamnatin Buhari ta rage kudaden ketare da take ba 'yan kasuwa saboda shigo da kaya daga kasashen ketare.
Wannan matakin da gwamnati ta dauka ya shafi kaya irinsu siminti da kajin turawa da kuma kifi.
Jihar Legas wadda ita ce cibiyar kasuwancin yammacin Afirka kuma mai tashoshin jiragen ruwa da na sama ta kasance cibiyar shigo da kaya daban daban.
Wakilin Muryar Amurka ya zagaya cikin birnin Legas domin jin dalilinsu da son sayo kayan ketare.
Wata 'yar kasuwa tace kayan da aka sarafa a kasashen ketare sun fi tsafta da inganci kuma 'yan kasan masu sayen kayan sun fi son na ketare. Kayan da ake yi a Najeriya yawancinsu mutanen Ibo ke yinsu kuma basu da inganci. Yawancin matan Najeriya sun fi son sayen kayan sawa daga Ingila ko Amurka ko Turkiya. Da wuya 'yan mata su sa kayan Najeriya.
Shi ma wani matashi sanye da kayan ketare yace kayan Najeriya basu da inganci ko bada sha'awa kamar na ketare. Kodayake 'yan Najeriya na son kasarsu to amma babu wanda zai so ya sa kayan da basu da inganci.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5