Nigeria Ta Chanza Ranaikun Gudanar Da Zaben Kasar

Wani mutum da ba'a tantance dashi bane ke karanta kanun labarun wata Jaridar da aka rubuta "an dai ji kuna", bayan da shugaban hukumar zaben Nigeria Attahiru Jega ya bada sanarwar dage gudanar da babban zabe, jiya lahadi, 3 ga watan Afrilun shekarar 2011

Hukumar zaben Nigeria ta dage tare da sauya ranaikun gudanar da babban zaben da aka shirya yi a kasar. Dagewar farko anyi tane ran Asabar aka maida ranar zuwa Litinin. A ran lahadi kuma sai hukumar ta sake bada wata sabuwar sanarwar dake cewa, yanzu za’a gudanar da zaben ‘yan Majalisa ran 9 ga watan Afrilu, sannan a gudanar da zaben shugaban kasa ran 16 ga watan Afrilu na gwamnoni kuma ran 26 ga watan Afrilu.

Hukumar zaben ta Nigeria, ta bada hujjar daukan matakin yin sauyin ne saboda matsalolin da aka samu wajen rarraba kayan gudanar da zaben.A wata tattaunawar da yayi da manema labarai ran lahadi, shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega yace masu ruwa da tsaki a zaben sun nemi a kara dage lokacin gudanar da zaben.Amma dagewar ta jawo bacin rai da takaici a Nigeria,kuma hukumar zaben Nigeria na fuskantar suka daga ‘yan Nigeria masu jefa kuri’a.

Kafin ranar da aka fara shirya zaben farko ta Asabar, shugaban hukumar zabe Jega bai ankara da samun wata matsala ba, a maimakon haka ya ce zaben na Afrilu zai bai wa ‘yan Nijeriya damar daidaita matsalolin da su ka biyo zaben 2007, wanda tashe-tashen hankula, da magudi da rudami su ka dabaibaye zaben.