Wata kungiyar mai yaki da cin hanci da rashawa,tana zargin wasu Bankunan Britaniya biyar da karbar miliyoyin dala daga hanun baragurbin ‘yan siyasa a Najeriya.
Kungiyar mai suna “Global Witness” a turance, ta ce bankunan sun karbi ajiyar daga hanun tsoffin gwamnoni biyu,wadanda ake zargi da samo kudaden ta cin hanci da rashawa.
Kungiyar tace ajiyar da aka yi tsakanin 1999 zuwa 2005, ya janyo ayar tambaya kan kudurin Bankunan na yaki da kudaden haram. Daya daga cikin bankunan da ake zargi “HSBC” yana ikirarin ya shimfida sharudda da zasu hana irin haka aukuwa.
Sauran bankunan da kungiyar “Global Witness” take zargi sun hada da Barclays,NatWest,UBS,da kuma Royal Bank of Sctoland. Gwamnoni da ake zargi a wan nan dambarwar sune tsoffin gwamnoni Joshua Dariye na Jihar Plateau,da kuma Dieypreye Alamieyeseigha, na Bayelsa.
Kungiyar mai yaki da cin hanci da rashawa tace rahotonta ya dogara ne kan bayanan kotu da gwamnatin Najeriya ta gabatar na neman a mayar mata da kudaden.