Sabon Fada Ya Barke A Jos

A wan hoto mutane da suka jikkata a harin boma bomai da aka kai a Jos ranar jumma'a suke kwance a gadajen asibiti.

Sabon fada ya barke a Jos yau lahadi,kwana biyu bayan harin boma bomai da ya kashe mutane 32 cikin birnin.

Sabon fada ya barke a Jos yau lahadi,kwana biyu bayan harin boma bomai da ya kashe mutane 32 cikin birnin.

Shaidu sun bada labarin an cunnawa wasu gine gine wuta a fada da ya barke tsakanin kiristoci dauke da makamai da wasu kungiyoyin musulmi. An tura jami’an tsaro domin shiga tsakani,yayainda ake ganin hayaki ya cika yankin.

Akwai rahotanni da ba’a tabbatar ba cewa an raunata wasu mutane a fadan na yau lahadi.

Jiya Asabar,shugaba Goodluck Jonathan ya yi alkwarin gwamnatinsa zata yi farautar wadanda suke da hanu a kai wan nan hari ranar jumma’a.

Da yake magana a bainar jama’a,Mr.Jonathan yace gwamnati zata yi amfani da duk ikonta wajen “gano”,wadanda suke da hanu a kai harin da ya halaka mutane.