Babu fasinja daya da ya tsira, cikin motocin biyu duka,da suka kama da wuta bayan hadarin. Motocin duk sun kone kurmus kamin 'yan kwana kwana su zo.
Jami’an Najeriya sun bada labarin an yi hadarin motocin fasinja biyu, akalla mutane 33 sun halaka. Wani dogarin hanya,Boyi Ali Maigari, ya gayawa manema labarai yau Talata cewa, motocin kiya kiyan duka biyu sun kama wuta bayan hadarin,kuma fasinjoji dake ciki sun kone kurmus. Hadarin mota ba sabon abu bane kan hanyoyi Najeriya da ba’a gayara su.