Zaman Kotu a Bainar Jama'a a Nijar

Babban Alkalin Kotun Yamai dake Niger, Ibrahim Haruna

A kowace shekara babban kotun kasar Niger ya kan yi zama a bainar jama'a ya saurari manyan laifuka tare da yin hukunci domin ya zama darasi ga jama'ar kasar don su guji aikata irin laifukan.

Kimanin kararraki 38 da ke kunshe da laifuka daban-daban ne ke gaban alkalan kotun da za ta zauna a bainar jama'a a birnin Yamai da nufin ba da daratsi ga al'ummar kasa.

Shugaban kotun daukaka kara na birnin Yamai mai shari'a Ibrahim Haruna shi ke jagorancin zaman wanda ya ce " zama ne wanda za'a yi shari'a bisa ga manyan laifuka". Manyan laifukan sun hada da kisan kai, fyade, sata, har da ta makami.

A cewar alkalin shari'ar da zasu yi ba takardu ba ne zasu tsaya suna duba wa. A'a, zasu tambayi wadanda ake zarga da laifukan su bayyana yadda lamarin yake tare da bincika rayuwarsu.

Sabanin abun da ya faru bara, a zaman kotun na wannan shekara lauyoyi zasu kasance a kotun saboda kungiyoyin lauyoyi ta ce ta fahimci wasu mahimman abubuwa kamar yadda wani lauya Maitir Mamman ya fada.

Mamman ya ce idan babu lauyoyi cikin shari'a ba za ta yiwu ba. Ta dalilin haka ne kungiyarsu ta yanke shawarar kasancewa a kotun duk da rashin biyansu alawus alawus kamar yadda doka ta tanada.

Hukumomin shari'a na cewa gwamnatin Niger na yin iyakacin kokarinta domin ta ga cewa kowace jiha ta yi irin wannan zaman na musamman a kowace shekara.

Mai shari'a Musa Doma Hamidu daraktan harkokin shari'a a ofishin Ministan Shari'a ya ce su na kokari su ga an yi irin wannan shari'ar a kowace jiha tare da samun lauyoyin da zasu tsayawa mara sa halin daukan nasu lauyoyin.

Gudanar da irn wannan shari'ar nada tasiri saboda dabi'ar yada jarirai cikin kwalbatoci da aka saba gani akai akai saboda wasu dailai masu nasaba da al'adu ta fara raguwa. Amma kisan kai da fyade sun fara kamari a Niger.

Ga rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

NIGER: Zaman Kotu a Bainar Jama'a Na Shekara-shekara - 3' 03"