NIGER: Yau Ce Ranar Cutar Zangai Ta Karnuka Ta Majalisar Dinkin Duniya

Hukumar kiwon lafiyar dabbobin Nijar ce ta kaddamar da yiwa karnuka gwajin cutar zangai a cikin shirin ranar yaki da cutar ta Majalisar Dinkin Duniya.

An kaddamar da kemfen din yaki da cutar zangai ta karnuka a jihar Damagaran ta Jamhuriyar Nijar a cigaba da tunawa da ranar yaki da cutar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe, wato,kowace ranar 28 ta watan Satumbar duk shekara.

Dr. Abdu Isiyaku babban darakta a ofishin kiwon lafiyar dabbobi na Jamhuriyar Nijar yana mai cewa hukumar Majalisar Dinkin Duniya ce ta tsayar da ranar. Tana ce da za'a kula da cutar zangai da kan kama karnuka har ta kaisu ga mutuwa ko kuma wadanda suka ciza.

A wannan ranar za'a yiwa mutane bayanin wayar da kawunansu tare da yiwa karnukansu gwaji kyauta da kuma ba duk karen da aka sameshi da cutar maganin warkar dashi. Burin ma'akatar shi ne kawar da cutar domin tana kashe dabbobi da mutane.

Baicin yiwa karnuka gwaji za'a wayar da kawunan jama'a kan matakan da suka dace su dauka domin kawar da cutar.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar da Ranar Kulawa da Cutar Zangai Ta Karnuka Ta Majalisar Dinkin Duniya a Nijar - 3' 22"