Jam'iyyun siyasa sun ce su har yanzu bata canza zani ba a jihar. Gwamnatin jihar ba'a san inda ta sa gaba ba.
Shugaban jam'iyyar APGA na jihar Musa Aliyu Liman ya kira taron manema labarai inda ya bayyana rashin gamsuwarsu da kamun ludayin mulkin APC a jihar. Yace jama'ar jihar sun san sun ba gwamnatin gudummawa da goyon baya. Yace su 'yan takara sun sauka domin a samu canjin gwamnati lamarin da ya sa APC ta samu nasara.
Tun farko talakawa suna neman canji daga mulkin PDP. Saidai yace abun bakin ciki ne a ce har yanzu basu san inda sabuwar gwamnatin ta sa gaba ba. Akan gyaran hanyoyi da sabuwar gwamnatin tace ta yi Liman yace tsohuwar gwamnati ce ta fara bata gama ba kafin karshen wa'adinta. Aikin da aka soma suka ci gaba dashi.
Aliyu Liman yace rabon taki ya zama wani abu yanzu a jihar. Idan mutum baya jam'iyyar APC ba zai samu taki ba balantana ya san yadda aka raba.
A bangaren PDP Malam Yahaya Abiliki mataimakin tsohon gwamnan jihar akan harkokin siyasa yace su har yanzu basu san an yi canji ba. Ba'a taimakawa matasa samun aikin yi ba. Ayyukan da gwamnatin keyi na gwamnatin PDP take karkarewa.
Shi kuwa Injiniya Muhammad Imam shugaban APC na jihar cewa yayi sun cigaba da yin aikin da tsohuwar gwamnati ta fara saboda bata biya kudin aikin ba. Su ne suka biya yanzu.
Kakakin gwamnan jihar Dr Ibrahim Doba ya mayarda martani game da batun rabon taki. Yace ya je wata karamar hukuma ya gani kuma rashin kawo takin da wuri ne ya janyo cecekucen.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5