NIGER: Shugaban Jam’iyyar MPR Jamhuriya Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Siyasa Domin Kubutar da Kasarsu

Shugaban Nijar, Issoufou Mahamadou

Yayinda jam’iyyar MPR Jamhuriya ke bikin cikar shekaru biyu da kafa ta, shugabanta, Albade Abuba, yayi kira ga ‘yan adawa da masu rinjaye su manta da banbancin siyasa domin su kubutar da kasar daga halin fatara da matsalar tsaro

A jajiberen zaben 2016 ne wasu jigajigan jam’iyyar MNSD suka kafa jam’iyyar MPR Jamhuriya bayan da suka yi shekaru biyu suna tafka shari’a tsakanin masu goyon bayan shugaban kasar Issoufou Mahamadou da wadanda suke adawa.

Yayinda jam’iyyar ke cika shekaru biyu da kafuwa, shugabar matan jam’iyyar, Madam Lamido Salamatu Bala Goga tace jam’iyyarsu ta taka rawar gani saboda watanni uku da kafata ta shiga zaben kasa har suka ci kujeru 13.

A bikin nata, jam’iyyar ta gayyato shugabannin siyasar kasar baki daya lamarin da ya ba shugabanta Albade Abuba damar kiransu da su kawar da banbancin siyasa su hada kai domin yakar matsalolin da kasar ke ciki yanzu irinsu fatara da tabarbarewar tsaro.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

NIGER: Shugaban Jam'iyyar MPR Jamhuriya Ya Kira Hadin Kan 'Yan Siyasa dDomin Kubutar da Kasar - 2' 51"