Jamhuriyar Niger, a yau 26 ga watan Satumba, na tunawa ranar da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta hannun hukumar kiwon lafiya ta kebe domin fadakarwa akan sa sarari tsakanin wannan haihuwa da waccan.
Malam Hassan Haruna mai kula da harkokin sadarwa a babban asibitin Birnin Konni ya bayyana mahimmancin wannan ranar ga al’ummomi, musamman malaman asibiti.
Malam Haruna rana ce ta sakin sarari tsakanin haihuwa domin rashin sakin sarari ya na kawo matsaloli da dama ga mata. ‘Ya mace na iya rasa rayuwarta ko kuma ta samu ciwon yoyon futsari da wasu cututukan. Rayuwar ta gaba daya na iya baci. Su na rokon maza su yi kokari su bar mata su yi anfani da asibiti. Kazalika su bar matan su su yi anfani da hanyoyin zamani na saka sarari tsakanin haihuwa.
Gwamnatin Niger ta fito da shirin kafa majalisu a cikin karkara domin ba mutanen karkaran damar su tattauna lamuran da suka shafi rayuwarsu, ciki ko har da saka sarari tsakanin haihuwa.
Wani mazauna karkaran yay aba da shirin saboda a can baya sai a ga mace da da yana zawo, ga wani kuma bai ma fara tafiya ba gashi kuma ta na da sabon ciki, lamarin da ya ce bai dace ba. Amma yanzu mata godiya su keyi dangane da fadakarwar da aka yi masu. Yanzu mahaifa tana hutawa yaro kuma sai ya yi karfi kafin a dauki wani cikin.
A saurari rahoton Haruna Bako domin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5