A daidai lokacin da dabbobi ke kwararowa daga arewacin Niger zuwa kudancin kasar domin yin kiwo bayan damina, kungiyar makiyaya ko Anpen ta shirya taron muhawara tsakaninta da manoma a Birnin Konni tare da hukumomin jihar Tahoua.
Manufar taron ita ce tunkarar duk wani abu da ka iya jawo tashin hankali tsakanin al’ummominsu.
Dr Usman Maila magajin garin Birnin Konni, yace taron faduwa ce ta zo dede da zama. Ya ce da zara an ce an kai karshen damuna sun shiga matasala ke nan tsakanin kungiyoyin biyu. Basa samun masalaha sai lokacin da manoma suka kammala girbin shukarsu kuma makiyaya sun wuce. Ya ce da ikon Allah ga makiyaya da manoma suna tattaunawa domin lalubo hanyoyin kaucewa ayyukan asha.
Malam Abdalla shugaban kungiyar makiyaya ya ce burinsu shi ne manoma da makiyaya su gane dokokin kasa kuma su bisu tare da rokon Allah ya kara masu kwanciyar hankali.
Shi kuwa Malam Ahmadu Habibu Halilu shugaban kungiyar Ropen da ta tallafawa kungiyar Anpen shirya taron ya ce sun yi hakan ne domin hada kawunan makiyaya da manoma da sarakuna da mahukuntan karkara a samu zaman lafiya
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5