Niger Delta Avengers Na Barazanar Komawa Kai Hare Hare Akan Bututun Mai

Mayakan Niger Delta

A bayan barazanar wannan kungiya cewar ba a cika alkawuran da aka yi mata ba, rundunar sojojin Najeriya dake yankin ta ce kungiyar ba ta fi karfin hukuma ba

Kungiyar 'yan bindigar Niger Delta da ake kira Niger Delta Avengers wadda ta yi kaurin suna wajen kai hare hare kan bututun mai da kamfanonin dake hakar danyen mai a yankin ta yi barazanar komawa kai hare hare akan bututan mai.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta aikawa manema labarai mai dauke da sa hannun wani da ya kira kansa Janar Maduch Abinebu. Sanarwar ta ce babu wani saurarawa kuma da zata yi. Ta sha alwashin tsananta kai hare hare cikin 'yan kwanaki masu zuwa a sassa daban daban inda ake hakan danyen mai. Bugu da kari kungiyar ta ce ta yi watsi da duk wani sulhu da gwamnatin tarayyar Najeriya.

A sanarwar kungiyar ta kara da cewa zata fito da wasu sabbin dabarun zamani domin fadada hare harenta kan kamfanonin ayyukan mai.

Mai magana da yawun rundunar sojin dake kula da yankin Manjo Ibrahim Abdullahi ya ce barazanar ba wata sabuwar abu ba ce. Ya ce kowa na iya zuwa yanar gizo ya fadin abun da yake so. Wanda ma ya fitar da sanarwar ba'a sanshi ba. Injishi, jami'ansu suna koina a yankin saboda tabbatar da tsaro. Manjo Ibrahim Abdullahi ya kara da cewa a yadda suke babu abun da ya fi karfinsu. Ya roki jama'ar yankin su dinga taimaka masu da bayanan sirri domin inganta tsaro.

Yayinda kungiyar ta ja kunnuwan kamfanonin mai dake aiki a yankin, wani dan yankin ya ce idan 'yan kungiyar suna aikata ta'addanci ita ma gwamnati tarayyar Najeriya tana da laifi kasancewa ta hada kai da kamfanonin dake hakan mai wajen bata masu muhallansu. Inishi bai kamata a saurari 'yan kungiyar ba saboda yin hakan bashi da amfani.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Niger Avengers Na Barazanar Komawa Kai Hare Hare Akan Bututun Mai - 4' 44"