Nicolas Pepe Ya Baiyana Dalilansa Na Shiga Kulob Din Arsenal

Dan wasan na Ivory Coast ya tabbatar da komawarsa zuwa kulob din Arsenala a cikin bazara, ya ce a gare shi ya yanke shawarar ne da za ta ba mutane mamaki, domin ba kungiya ce da ke gasar zakarun Turai ba, amma kuma kulob ne da ke da buri sosai.

Ya kara da cewa "duk da cewa na ji dadi, amma bana tunanin hakan ko kadan. Na zo Arsenal ne saboda ina da burin samun nasara, shi ya sa na zo.

Ya ci gaba da cewa "Ni, da kaina, abu ne da na saba mu'amula da shi a ko da yaushe, ‘yan uwana da abokaina, za su iya tunanin Yuro miliyan € 80m , amma a gare ni abu ne da na saba."

“Na kuma yi mamakin sosai, saboda na dadai cikin wannan al’amuran, don haka abin buri ne a gare ni. Abu ne wanda zan yi hanzari a gefe guda kuma in mayar da hankali kan kwallon kafa.

Pepe, wanda ke da tarihin nasaran zira kwallaye 23 cikin dukkan wasannin gasa a kakar wasannin da ta gabata, ya samu damar zaban daya daga cikin manyan kungiyoyin kulab din na Turai.

Lille ya yi tsammanin ya ga wadanda su ka nuna sha’awarsu da dama, amma yawancin mutane sun yi mamakin yadda kwararre kamar shi ya amince ya tafi kulob din da ba zasu iyaka kaiwa ga gasar Champion League ba.