Mutane Milyan Daya Ne Suka Cika Dabdalin Times Square A New Domin Bikin 2011

Ana ruwan furannin leda wadansu kuma suna wasannin kayatarwa a dandalin Times Square,lokacind ake dakon shigar sabuwar shekara.

Mutane suna sowa lokacinda aka fara sauko da kwallon nan mai haske,ana kidayar nan na dakikai miniti daya kamin sabuwar shekara ta kama.

Mutane milyan daya ne suka cika dandalin Time Square dake New York domin murnar shiga sabuwar shekara.

Mutane suna sowa lokacinda aka fara sauko da kwallon nan mai haske,ana kidayar nan na dakikai,minti daya kamin sabuwar shekara ta kama.

Nan da nan wasan wuta ya cike sararin samaniya birnin New York,sai aka ji mutane da babban sauti suna cewa “Barka da Sabuwar Shekara.”

Haka ma bukukuwa da aka yi a kasashe dake kudancin nahiyar Amurka,an kayatar da wasannin wuta a biranen Buenos Aires, Argentina, aka kuma ci gaba da yi har da asubahin yau domin shiga sabuwar shekara ta 2011.

Sa’o’I da dama kamin wadan nan bukukuwa anan Amurka kasashe dake Turai, Afirka, da Asiya da yankin Pacific suka yi nasu.

A Ingila ne aka yi biki mafi kayatarwa a Turai an yi bikin ne a gabar kogin Thames dake London.Kimanin mutane dubu metan da hamsin ne suka hallara domin kallon wasan wuta,yayinda babban agogon birnin London da ake kira "Big Ben" dake kan ginin majalisar dokokin kasar yake cas cas cas, da shigar sabuwar shekara.

Tunda farko ‘yan kasar New Zealand sun yi bikin shiga sabuwar shekara da wani kasaitaccen wasan wuta a birni Auckland, yayinda a birnin Sydney na Australia kuma,mutane milyan daya da rabi ne suka fito domin wasan wuta da aka saba yi a dai dai wan nan lokaci duk shekara, kan wata gada da ake kira Harbor.