Gurbatar yanayi a Birnin New Delhi cikin shekaru uku ya karu, wanda hakan ya tilasta dakatar da zirga-zirgan jiragen sama akalla 37 saboda rashin kyawun yanayi.
Gurbataccen hayaki mai sa hawaye, ya mamaye babban birnin na Indiya da wasu yankuna jiya Lahadi, wanda ya janyo mazaunan yankin suna hawaye da zafin idanu, ciwon makogoro, da kuma matsallar numfashi.
Fira Ministan Delhi, Arvind Kejriwal ya wallafa a shafin twitter cewa gurbatar yanayi ya kai inda ya kai, "ba mai iya jurewa" sannan ya yi kira ga gwamnatin da ta sa baki cikin lamarin.
“Gurbartar yanayi ta kai matakin da ba za a iya jurewa ba a duk faɗin arewancin Indiya. ‘Yan yankin New Delhi na cikin wani hali wanda ba laifin su ciki. Firayim Ministan ya nuna matukkar damuwarsa.
New Delhi, ne birni mafi gurbarta a duniya a cewar Greenpeace da AirVisual. Ana yawan samun ƙarin gurbartar muhalli a wannan lokacin shekara, kuma gurbartar iska na kara muni yayin da kusancin hunturu da manoma ke kokarin kona ciyawa. Haka kuma gurbartar yanayi na kara lalacewa saboda hayaki daga masu kuna banga a duk fadin yankin don murnar Diwali, wani babban biki na ‘yan Hindu.
Kananan hukumomin sun ba da umarnin a rufe makarantu da kwalejoji gaba daya har zuwa gobe Talata. An umarci direbobi a cikin birni wanda ke da sama da mutane miliyan 18 da kuma motocin masu rijista miliyan 8.8 da su bi tsarin raba hanya har zuwa ranar 15 na watan Nuwamba.