A jiya Alhamis a Nepal ma’aikatan agaji suka ceto wasu mutane biyu daga ‘baraguzan da girgizar kasar data faru karshen satin daya wuce, abun farin ciki na ba safai ba, yayinda adadin wadanda bala’in ya hallaka ya kusa kai 6,000.
An goce da sowa a Kathmandu babban birnin kasar lokacinda ma’aikatan agaji suka zakulo wani yaro ‘dan shekaru 15 daga cikin baraguzan gidan saukar baki. Bayan ‘yan sa’o’i kuma an samu nasarar ceto wata ma’aikaciyar a sashen girke girke na waniotel.
Matashin rufe da kura an saka masa abin rike wuya kafin a ‘dauke shi zuwa asibiti, amma ma’aikatan lafiya sunce matashin ya samu ‘yar kwarzana ne kawai. Yaron dai yace ya samu robar mai ‘dauke da manshanu, kuma ita ya dinga sha har akaceto shi.
Ma’aikatan agaji dai sunce matar da suka zakulotana cikin hayyacinta, har daya daga cikinsu yake cewa tana magana tamkar “tana jin kamar an sake wata sabuwar halitta”.
Tawagar masu aikin ceto daga kasashen duniya na cigaba da tono gine ginen da suka rushe, yayinda masu aikin agaji suke kokarin rarraba kayan masarufi ga wadanda suka tsira.