Kowace gwamnati ta zo sai ta dan tabo batun, tayi nata iya kokarin kafin maganar ta mutu ko tayi shiru kamar an shuka dusa.
A zamanin shugabantin Olusegun Obasanjo an taso ca kamar za'a yi wani abu yayin da majalisar dattawa ta kafa kwamiti domin yayi bincike akan yawan man da aka ce yana kwance a rewacin Najeriya.Haka maganar daga bisani ta mutu.
Sanata Salisu Musa Matori dan masanin Bauchi yana cikin wadanda suka yi bincike. Yace a bangaren Chad Basin wato a arewa maso gabas akwai rijiyoyin man fetur guda ashirin da uku. Kowacce cikinta an samu mai sai dai a kara zurfinsu domin akai inda za'a samu wadataccen man. Amma an yi alkawarin za'a dawo kuma ba'a dawon ba. A yankin Bauchi-Gombe akwai rijiyoyi guda uku da suka bada tabbacin mai da iskar gas. Iskar gas dake wurin ta isa ta ba duk arewa maso gabas wutar lantarki da ma'aikatun Kano da Kaduna.
Shi ma Sanata Suleiman Adoke yace duk da binciken da aka yi aka gano cewa akwai mai mahukuntar kasar sun yiwa al'amarin rikon sakainar kashi. Gwamnatin tarayya ce kadai take da ikon bada izini a hako mai a koina aka sameshi a kasar.
Sakataren dillalan man fetur na kasa Danladi Fasali yace tuni an ba dillalan izinin hakar mai amma a jihar Kogi. Yace tsoron zabe ne ya sa suka dakatar da aiki. Amma yanzu da aka gama zabe lafiya zasu fara aikin gadan gadan.
Ga rahoton Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5