Neman Kawo Gyara Yasa Aka Kafa Gidauniyar Sawaba

Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Aniyar kawo gyara kan yadda alamuran siyasan Najeriya ke wakana na cikin dalilan da suka sa aka kafa gidauniyar Sawaba.
Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna Abdulkadiri Balarabe Musa shi ya jagoranci wani taro da manema labarai gami da 'yan mazan jiya na jam'iyyun NEPU da PRP a Kano dangane da kafa gidauniyar Sawaba.

Tsoffin shugabannin NEPU da PRP basa jin dadin halin da Najeriya take ciki yanzu. Tun da suna da rai sun sha alwashin ba zasu bari abun ya wuce ba.

Balarabe Musa yace gidauniyar zata yi aiki ne akan manufofin NEPU da PRP. Manufofin kuwa su ne 'yancin dan Adam da dimokradiya da kafa gwamnati da zata yiwa jama'a anfani da hadin kan Afirka da kuma bada ilimi kyauta. Aikin da tsoffin jam'iyyun suka yi yanzu yana neman ya bace. Gidauniyar Sawaba zata sake farfado da manufofin ta sake sabuntasu.

Farfasa Dan Datti Abdulkadir na cikin wadanda suka bada gudummawa wajen kafa PRP a jamhuriya ta biyu. Yace abun da Malam Aminu Kano yayi yasa shi ya dage sai yayi ilimi. Yace tun ana binsu ana bugunsu har 'yan sarakuna suka shiga jam'iyyar suka hana noman dole. Da kafin ka noma gonarka sai an tilasta maka ka noma ta sarki.

Gidauniyar zata ilimantar da jama'a da kuma bada horo akan siyasa da shugabanci.

Alhaji Dauda Dan Galan daya daga cikin 'yan gwagwarmayar jam'iyyar NEPU yace sinadaran nasara ga gidauniyar Sawaba su ne a yi tsarin mulki wanda zai ba kowa 'yanci a cikinta. Ana bukatar shugabanni nagari da zasu gudanar da shirin gidauniyar. Dole a tabbatar da dimokradiya. A ayana sharuda kuma duk wanda ya keta sharudan da aka ayana dole a yi masa horo ba sani ba sabo.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Neman Kawo Gyara Yasa Aka Kafa Gidauniyar Sawaba - 3' 30"