Sabon Garin Borgu Na Jihar Neja Ya Cika Shekara 50

Sarkin Borgu cikin farar riga

Sabon garin Borgu da aka fi sani da New Busa ya cika shekaru 50 da kafuwa biyo bayan gina madatsar ruwan Kainji a dai dai tsohon garin. Bikin ya samu halartar sarkin Borgun da ‘yan majalisar jihar Neja dana tarayya da gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello

A jihar Neja an gudanar da biki domin cika shekaru hamsin da kafa garin Sabon Garin Borgu da ake kira New Busa a jihar Neja sakamakon gina madatsar ruwan Kainji a daidai inda tsohon garin Borgu yake.

Gwamnatin farar hula a lokacin Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ne ta gina madatsar ruwan da manufar kafa tashar samar da wutar lantarki.

Yanzu alkalumma sun nuna cewa kashi 80 cikin 100 na garuruwan dake zagayen madatsar ruwan basu da hasken wutar lantarki. A wani gefen kuma suna fama da kayan more rayuwa.

Ahmed Baba Suleiman shugaban karamar hukumar Borgu y ace akwai wasu kauyukan da dole aka dagasu zuwa wani wurin sanadiyar madatsar ruwan amma basu anfana da wutar lantarkin ba.

Mai martaba Sarkin Borgu Alhaji Muhammadu Sale Haliru Dantoro y ace duk da yake an samu ci gaba a yankin masarautarsa cikin shekaru 50 da suka gabata amma akwai bukatar gwamnati ta kara maida hankali a yankin. Ya bukaci a gyara masu hanyoyi tare da basu filin jirgin sama domin inganta harkokin sufuri tare da habaka kasuwanci.

Daya daga cikin ‘yan asalin yankin Sanata Aliu Sabi Abdullahi wanda kuma shi ne Baraden Borgu, injishi bisa gwargwado an samu ci gaba amma yana neman a yi masu hanya daga Borgun zuwa Rofiya da hanyar Kayama da Ruwan Busa.

Barrister Mukhtar Ibrahim Na Sale wanda aka haifeshi shekarar da aka kafa garin yace shi ne na farko da aka fara haihuwa a duka kasar kuma ya yi munar ranar.

Shi ko gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello da ya kasance a taron y ace suna kokarinsu wajen samar da ababen more rayuwa a yankin Borgu soboda sun gama aikin hada wuta a wasu wuraren yankin suna jira ne kawai a yi gwaji kafin a fara anfani da wutar.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Garin Busa, New Busa, A Jihar Neja Ya Cika Shekaru 50 Da Kafashi - 3' 07"