LAGOS, NIGERIA - Shugaban hukumar NDLEA General Buba Marwa mai murabus ya ce hodar ta iblis da aka kama a makon jiya a anguwar Ikorodu, farashin ta a kasuwan bayan fage zai kai na Dalar Amurka miliyan 278,250,000 kwatankwacin Naira biliyan 194,775,000,000.
Janar Buba Marwa, wanda Daraktan sharia na hukumar Mr. Sunday Joseph ya wakilta, ya godewa hukumomin yaki da safarar muggan kwayoyi na kasa da kasa musamman na Amurka bisa goyon bayan da suka baiwa hukumar da bayanan sirri da su kai ga kama wannan hoda ta iblis da ke zama mafi yawa da hukumar ta taba kamawa tun lokacin da aka kafa ta.
Barrister Abubakar wanda shi ne kwamandan hukumar ta NDLEA mai lura da kan iyakan Najeriya da Jamhuriyar Benin a SME border kuma yayi karin haske game da kwayoyin da aka kona.
Ya ce wannan ita ce kwaya mafi yawa da aka kama, kuma yawancin wadannan kwayoyi na da nasaba da ayyukan ta’addanci da ke faruwa a kasa, kuma suna yabawa da ayyukan shugaban hukumar bisa namijin kokari da ake yi tare da kira ga jama’a, da su tallafa da bayanan sirri wajen samun nasara a wannan yaki da fataucin muggan kwayoyi a kasa.
Ita ma a bangaren ta Madam Patricia Afolabi, Darakta a bangaren binciken kwakwaf na hukumar NDLEA ta ce bayyana illar dake tattare da shan muggan kwayoyi musanan hodar Iblis da dai sauran su zai taimaka, tayi kuma kira ga hukumomi da iyaye dasu tashi tsaye wajen raba matasa da mu’amala dashi.
Ko da yake, an kai wadanda aka kama wadannan kwayoyi wajen da aka kona, amma ba’a bari ‘yan jaridu suka yi hira dasu ba, domin kuwa yanzu haka suna fuskantar shari’a ne a gaban kotu.
Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibrin:
Your browser doesn’t support HTML5