NDLEA Ta Kama Makaho Dan Nijar Da Ake Zargi Da Safarar Miyagun Kwayoyi

Tabar wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama Bukar Haruna da dansa Saka Haruna da su (Facebook/NDLEA).

NDLEA ta kama makahon da dansa ne a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya a lokacin da suke kokarin komawa Nijar.

Jami’an hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta NDLEA, ta ce ta kama wani mutum makaho da dansa yayin da suke kokarin safarar tabar wiwi da miyagun kwayoyi.

An kama mutanen biyu ne a hanyar Malumfashi-Zaria a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya kamar da hukumar ta NDLEA ta wallafa a shafinta na Facebook dauke da sa hannun Darektan yada labaran hukumar Femi Babafemi.

NDLEA ta ce an samu Bukar Haruna, wanda shi ne makahon mai shekaru 52 da dansa Saka Haruna mai shekaru 30, dauke da kilo 20.5 na tabar wiwi da kuma gram 10 na exol-5.

Hukumar ta NDLEA ta kara da cewa asalin mutanen sun fito ne daga jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar.

Bukar Haruna da dansa, na hanyarsu ta komawa Nijar ne a lokacin da jami’in hukumar ta NDLEA da ke sintiri suka cafke su.