Kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafara a Kudu maso gabashin Najeriya ta ayyana dokar zama gida a ranakun Litinin da Talata na makon jiya, inda kuma ta ci gaba da aiwatar da dokar a wannan makon a ranakun na Litinin da Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kungiyar ta IPOB sun kuma kai farmaki a wata makarantar sakandare a jiya Litinin, kan wasu dalibai da suka bijirewa dokar suka fita domin rubuta jarabawar kammala babbar sakandare.
To sai dai kuma babbar kungiyar 'yan kabilar Igbo ta Ndigbo Ohanaeze, ta ce wannan lamari na kokarin kassara yankin ta haujin tattalin arziki da kuma sha'anin ilimi.
Wata sanarwa da ta sakataren kungiyar ta Ohanaeze, Mazi Okechukwu Isiguzoro ya fitar, ta bayyana cewa wannan dokar ta sabawa al'adar 'yan kabilar Igbo da aka sani da fafutukar neman arziki da ilimi.
"Mun damu sosai da wannan rashin hankali da ke kokarin wargaza rayuwa da ilimin yaran Igbo masu tasowa; akwai takaici yadda 'yan wasu kabilar ta Igbo suke halayya kamar masu son durkusar da Igbo," a cewar sanarwar.
A bangaren tattalin arziki kuma, Ohanaeze ta ce dokar zaman gidan ta haddasa asarar zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan 3.8 a yankin na Kudu maso gabas.
Akan haka kungiyar ta yi kiran da tilas a kawo karshen wannan dokar da ta bayyana a matsayin "rashin hankali".
Ohanaeze ta bayyana cewa tana goyon bayan gwamnonin jihohin yankin na sake garambawul ga shugabancin kungiyoyin 'yan kasuwa musamman wadanda ke goyon bayan dokar ta zaman gida ta IPOB.