Na'urar Tantance Katin Zabe Tayi Gardama a Sokoto

Tun da missalin karfe shida na safiyar yau wasu rumfunan zabe suka fara cika da batsewa da masu jefa kuri’a a jihar Sokoto, inda suka fara janlayi tun kafin isowar malaman zabe.

Ba tare da bata lokaci ba aka fara tantance mutane a mafi yawan rumfunan zaben jihar a cewa wakilin Muryar Amurka Ummar Faruk Sanyiina dake jihar ta Sokoto.

Wani malamin zaben ya shaida wa Faruk cewa komai yana tafiya dai, ya kuma ce babu jami'an tsaro a lokacin da suka fara aiki a wurin amma jama’ar wurin sun basu hadin kai sosai. Fatan dayawa da ga cikin masu jefa kuri’ar shine ayi zabe lami lafiya.

To sai dai kamar wasu jihohi da suka fuskanci matsalar na’urar nan ta tantance katin zabe, a jihar Sokoto ma na’urar ta yi gardama, inda ta ki karanta yatsaun wasu jama’a abinda ya so ya kawo cece-ku-ce tsakanin jami’ai da masu zabe a wasu mazabun.

Kamar yadda shugaban hukumar zaben kasa yayi bayani, tuni wasu jami’an zaben suka bi wata hanyar tantance masu kada kuri’a amma ana kyautata zaton cewa zaben na yau na iya kai dare musamman a birane, sakamakon tururuwa da jama’a suka yi wanda har ya zuwa lokacin kada kuri’a ba a gama tantance wasu ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Zabe a jihar Sokoto - 3'03"