Ci gaba da kiran shugaban Buhari ya hukumta jami’an dake da hannu wajen yiwa fararen hula kisan gila da sunan yaki da ‘yan ta’adda, da hakan ke zuwa lokacin da hare haren ‘yan kunar bakin wake da danna boma bomai ke kara karuwa na tado Karin bukatar mutane su rage tsoro wajen kula da shiga da ficen wadanda basu yarda da take taken su ba.
Shugaba Buhari dake ziyara a kasa ta ukku dake cikin rundunar yaki da Boko Haram, wato Kamaru, na karfafa batun daukar matakan hana ta’addanci daga kan iyakokin kasashen dake makwabtaka da tafkin Chadi.
Masana na nuna ‘yan ta’adda sun watsu zuwa garuruwa a halin yanzu da hakan ke kawo Karin hare haren sari ka noke.
Da yake nazartar lamarin ta hanyar aikin Inginiya tsoho shugaban matatar main a Kaduna Kailani Muhammad, na ganin sauya dabarun tsaro a yankunan taruwar jama’a zai fi sama mafi a’ala.
Yace naurorin zamani masu dago mai dauke da kayan fashewa tun daga nesa shi ake bukata a wuraren ibada da wuraren cunkoson jama’a.
Suma saura fararen hula masamman ma maharba na ganin zasu ci gaba da tallafawa jami’ai wajen sintiri a biranai da dazuzzuka dan magance kalubalen tsaron .