Wannan shirin da ya hada tarin jiragen ruwan yaki na kasashen duniya da dama da suka hada da na Amurka da Turai, na daya daga cikin matakan da suka samu nasara da aka dauka don maganin masifar barayin teku da suka addabi mutane a wasu shekarun baya.
A lokacinda barayin tekun ke shake ayarsu a can baya, ance sun saci dukiyar da ta kai ta zunzurutun kudi kamar Dala milyan dubu 7, kuma sunyi garkuwa da mutane sunfi dubu daya.
To amma rahottani sunce yanzu abin ya ragu matuka, don rabon da ace anyi wata gagarumar sata a cikin teku tun shekarar 2012; wannan ragi ne babba idan aka yi la’akari da cewa tsakanin shekarun 2010-2011, an kai farmaki akan jiragen ruwa sun fi 30.
Yanzu rahottani sunce NATO zata maida hankalinta ne zuwa tekunan Bahar Aswad da Mediterranean don tinkarar Rasha da kuma masu aiyukkan fasa kwabri a cikin tekunan.