Nasarar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Kafa EFCC Da ICPC A Kananan Hukumomi: Ekweremadu

EFCC

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu ya bukaci a kafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICPC a jihohi da kanana hukumomin Najeriya

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan ya furta haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a jami’ar Ibadan.

Sanata Ekweremadu, yace yaki da cin hanci da rashawa ba zai yi aiki ba sai an bashi mahimmanci na masamman yakamata a kafa hukumomin EFCC da ICPC a jihohi da kanann hukumomi da kafa ‘yan Sandan jihohi da hukumar da’ar ma’aikata da kotu masamman a kowace jiha da kananan hukumomi idan aka yi haka yaki da cin hanci da rashawa zai kan kama daga tushe.

Ya kara da cewa kafa wadannan hukumomi a jihohi da kananan hukumomin Najeriya shine zai sa hakar ta cimma ruwa ta inda za a ga tasirin yakin da ake yi da ci hanci da rashawa a Najeriya.

A nasa jawabin Farfesa Idowu Olayinka, cewa yayi saka kudi a fannin ilimi yana da mahimmanci saboda haka yakamata gwamnatin tarayyar Najeriya, ta kara zuba kudi a fannin.

Your browser doesn’t support HTML5

Nasarar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Kafa EFCC Da ICPC A Kananan Hukumomi: Ekweremadu - 2'05"