Dole kowa ya tabbatar an tattake cin hanci da rashawa soboda shi ne yake cima Najeriya tuwo a kwarya.
Farfasa Isah Radda ya gabatar da wata kasida a taron da cibiyar horas da mutane da kuma samarda ayyukan yi da ta gudanar a Kaduna akan illar cin hanci da yadda za'a yakeshi.
Farfasa Radda yace idan aka ci nasara akan cin hanci da rashawa Najeriya zata canza. A cikin kasidar da ya bayar ya lissafa hanyoyi da yawa da za'a bi a kawar da cin hanci da rashawa.
A bi hanyoyin a tabbatar cewa canjin da aka samu ya anfani al'umma yau da gobe. Idan aka shantake aka ki a kyautatawa al'umma to gaba fa ta fi baya yawa. Idan an zo wani zaben za'a shiga wata rigima daban.
A tashi tsaye a yi fada da cin hanci da rashawa. Yace a Najeriya duk aikin da za'a yiwa al'umma muddin ba'a shake wuyan cin hanci da rashawa ba to ba'a yi komi ba. Ba za'a ga tasirin duk kudin da za'a zuba a wani shiri ba idan an bar cin hanci da rashawa.
Farfasa Radda yace aikin gyaran kasa na kowa ne. Ba na jami'an gwamnati ba ne kawai.
Malam Muhammad Ali shugaban cibiyar da ta shirya taron ya bayyana makasudin shirya taron. Makasudin taron shi ne a wayar da kawunan mutane su san ma'anar cin hanci da rashawa saboda a hada karfi da karfe a yaki annobar.
Gwamnoni su ji tsoron Allah su bi doka. Idan sun yi hakan to kowa ma zai bi doka.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5