Nan ba da jimawa ba na’urorin zamani za su maye gurbin mafi yawan ayyukan yanzu, yayin da mafi yawan ayyukan yanzu babu su a shekaru goma da su ka shige.
ina bukatar sana’ar da ta dace da ra’ayi na, don haka na zabi aikin gine-gine.
Jennail Chavez 'yar shekaru 25 ta ce, kalubalen rayuwa ne kawai ya kaita ga shiga makaranta, mai cike da hargitsi iri-iri. Da fari, ta fara aiki ne da wani wajen ajiyan kaya, daga baya ta yi tunanin komawa makaranta ne ya fi mata. Bayan ta kammala karatun ta a kwalejin na shekaru biyu na aiki hanu a jihar Los Angeles, Chavez ta na san ran ta zama ‘yar kwangila. Kuma da yake ita mai son aikin hanu ce, kasancewar zaben aikin da maza su ka fi yi, bai bata tsoro ba.
Chavez ta ce, “ina bukatar sana’an da ya dace da ra’ayi na, don haka na zabi aikin gine-gine.”
Sai dai Chavez ta lura abunda take da shirin yi, nan ba da jimawa, na’urori zamani za su maye gurbinshi.
Shugaban kwalejin aikin hanu na Los Angeles, wato Los Angeles Trade Technical College, Laurence Frank, ya ce sabunta dabarun zamani na da muhimmanci ta fuskar cigaban tattalin arziki. Ya kara da cewa ya kamata ma’aikata su rika sabunta kwarewa da dabarunsu, dai-dai da zamani domin fuskantar fasahar zamani.
Sai dai Frank ya ce na’urori ba za su iya maye gurbin ayyuka da ke bukatar zunzurutun aiki da tunani ba. Ayyuka masu bukatar warware wata babbar matsala, ko daukan wani muhimmin mataki cikin hikima, kamar aikin hada ruwan gida, aikin lantarki za su cigaba da wanzuwa.
Haka rashin aikin ba zai shafi wasu kwarewa masu sauki ba kamar Sadarwa, aiki da lokaci, da kuma dabaran aikin hadin gwiwa.